|
||||||||||||||||||||||
|
Hukunce-Hukuncen AlwallaMas'ala ta 304:Wanda ya yi shakkak a cikin daya daga cikin sharudda ko ayyukan alwalla, kamar ya yi shakka a kan kasancewar ruwa mai naijasa ne ko kuma cewa na kwace ne,anan ba zai kula da shakkunsa ba. Mas'ala ta 305: Idan mutum ya yi shakka kan bacin alwalla ko rashib bacinta,anan zai yi hukunci akan ingancin alwallarsa.Amma idan bayan ya yi fitsari bai yi Istibra,I ba sai ya yi alwalla sai ya ji wata lema ta fito daga gare shi wadda bai sani ba shin fitsri ne ko wani abu daban,anan alwallarsa t abaci. Mas'ala ta 306:Wanda yake shakku akan cewa shin ya yi alwalla ko bai yi ba,anan zai yi hukunci ne da bai yi ba. Mas'ala ta 307:Wanda ya yi alwalla kuma yana shakka akan cewa ya aikata daya daga cikin abubuwan da ke bata alwallako a'a.Sanan kuma yana shakka shin kafin alwalla ne ko bayan alwalla, idan ya kasance kafin ya yi salla ne dole ya sake alwalla sannan ya yi salla, idan kuma ya zamana cikin salla ne, anan sai ya yanke sallar ya yi alwalla sannan ya sake kabbara sallar daga frko,Idan kuma ya riga ya yisallar,anna sai ya yi alwalla ya sake sallar da ya yi. Mas'ala ta 308:Idan mutum ya yi bayan ya yi salla sai yake shakka akan cewa ya yi alwalla ko bai yi ba, sannan kuma ya san cewa lokacin da ya fara salla hankalinsa na nan, anan sallarsa ta inganta.Amma dole ne ya sake alwalla don yin salla ta gaba. Mas'ala ta309: Idan mutum yana cikin salla sai yake yin shakka kana cewa shin ya yi alwalla lo bai yi ba,sallarsa ta baci dole ne ya yi alwalla ya sake salla. Mas'ala ta 310: Idan mutum bayan ya yi salla sai yake shakka shin kafin ya yi salla alwallarsa ta baci ko bayan ya yi salla ne,anan sallarsa ta inganta. Mas'ala ta 3011: Idan mutum ya kasance yana da rishin lafiya ta yadda ba ya iya rike fitsari ko kashi, Idan ya zamana zai samu dammar da zai yi salla daga farkon lokacin salla har zuwa karshen lokaci ta yadda zai yi alwalla ba tare da yana jin fitsari ko kashi ba, to anan ya wajaba ya aiwatar da sallarsa a wanannan lokacin.Haka nan idan ya zamana lokacicn kawai zai ishe shi ne ya yi ayyukan da suke wajibi a cikin salla, annan su kawai ya wajaba ya aiwatar, ya bar wasu abubuwan da wajibi ba ne kamar kiran salla, ikama da kunut. Mas'ala ta 312:Idan kuwa ya zamana ba ya samun lokacin da zai isa ya yi salla ta yadda bai ji fitsari ba, anan idan ba zai zama matsala bag are shi, sai ajiye ruwa kusa da shi ta yadda day a ji fitsari ya zubo sai ya sake alwalla sannan ya cigaba da sallarsa daga inda ya tsaya.Haka nana idan yana da matsala ta yadda zai ya yiwuwa kashi ya fito masa sau da yawa a cikin salla anna ma sai ya ajiye ruwa kusa da shi duk loakcin day a fito ya sake alwalla sannan ya cigaba da sallarsa. Mas'ala ta 313:Wanda yake da ciwon zubar fitsari, idan ya kasance zai iya salla guda biyu ba tare da fitsari ya fito ba, yana iya yin sallar guda biyu da alwalla daya, koda wani abu ya dige masa tsakanin sallolin biyu ba matsala,duk da yake dai abin da ya fi shi ne ya kiyaye. Mas'ala ta315:Idan ya kasance mutum ba zai iya yin alwalla ba sannan ya iya yin salla ba tare da kashi ya fito masa ba, anan yana iya yin salla da yawa da alwalla guda daya,sai dai idan cikin zabinsa ya yi kashi ko wani abu da ke karya alwalla. Mas'ala ta 316:Idan mutum ya kasance yana da rishin lafiya ta yadda ba zai iya rike tusa ba,anan sai yi aiki da hukuncin wadan da ba su iya rike kashi,kamar yadda muka fada a sama. Mas'ala ta 317: Wanda baya iya rike kashi dole ne ya yi alwalla gabanin kowace salla, sannan ba tar da bata lokaci bay a aiwatar da sallar.Ammam idan yana so ya rama sujjadar da ya manta a cikin salla ko tashahud, idan ya zamaza zai rama sun e bayan salla ba tare da bata lokaci ba, anan ba sai ya sake alwalla ba don aiwatar da su. Ma'sala ta 318:Wanda fitsarinsa yake fito digo digo, dole ne yayin salla ya sanya wani abi wanda zai tare fitsarin ta yadda kada ya taba wani wur daban daga cikin jikinsa.Sannan ihtiyati wajibi, shi ne ya canza wannan abin da ya yi amfani da shi don tare fitsarin idan zai gabatar da wata sallar.sannan kuma ya wanke alaurarsa inda fitsarin ya bata.Haka nan wanda ba ya iya tare kashi ta yadda bazai iya aiwatar da salla ba tare da kashin ya fito ba,ihtiyat wajib shi ne, idan ba zai zama wahala ba gare shi.dole ne ya wanke wurin da ka shin ke fitowa bayan kowace salla kafin ya gabatar da wata sallar. Mas'ala ta 319:Wanda ba iya tare kashi da fitsari,Idan zai yiwu ya yi kokari ya tare kashi da fitsarin yayin salla,ko wannan zai janyo kashe kudi,haka nan idan ya zamana zai iya yiwuwa a magance cutar,kuma zai iya yi wa kansa maganin cutar dole ya yi wa kansa magani. Mas'ala ta 320:wanda ba iya tare kashi da fitsari,sai wannan cutar ta warke bayan wani lokaci sallolin da ya yi lokacin da yake da wannan cutar,idan ya yi aiki da hukunce-hukuncen da suka hau kansa a lokacin, ba sai ya sake sallolin da yai ba a lokacin da yana da wannan cutar.Amma idan yana cikin salla sai wannan cutar ta warke sai ya sake wannan sallar.
|