|
||||||||||||||||||||||
|
Abubuwan da suke dole sai da alwalla:Mas'ala ta 321:Alwalla tana wajaba don yin abubuwa guda shida: 1-Don yin Salla ta wajibi ban sallar gawa. 2-Don yin sujjada ko tashahhud na ramuwa, idan zamana bayan sallar kafin ya rama su sai ya yi abin da yake karya alwalla. 3-Don yin dawafi a dakin Ka'aba. 4-Idan mutum ya yi alwakwali ko rantsuwa akan zai yi alwalla. 5-Idan ya yi bakance(alkawali)a kan zai taba rubutun kur'ani da wani bangaren jikinsa. 6-Idan mutum zai wanke kur'ani da ya taba najasa,ko fito da shi daga cikin najasa kamar bayan gida,amma wannan yayin day a zama dole sai hannunsa ko wani bangaren jikinsa sai ya taba kur'anin,amma idan ya zama tsayawar da zai yi don ya yi alwalla zai zama kamar rashin girmamawa ga kur’anin yana iya dauko shi daga bayan gida ba tare da alwalla ba,haka nan idan zai wanke kur’anin day a taba najasa idan yana wanke shi ba tare day a taba rubutun kur’anin ba yana iya wanke shi ba tare da alwalla ba. Mas’ala ta 322:shafar rubutun kur’ani ko taba rubutun kur’ani da wani bangare na jikin mutum ba tare da alwalla ba haramun ne.Amma idan aka fassara kur’ani da wani harshe ana iya taba shi ba tare da alwalla ba. Mas’ala ta 323:ba dole ba ne a kare karamin yaro ko mahaukaci daga taba rubutun kur’ani,amma idan ya zamana sakamakon taba shi da suka yi za’a iya lissafa shi daga cikin rashin girmama kur’ani dole ne a hana su taba kur’anin. Mas’ala ta 324:wanda ba shi da alwalla ihtiyati wajib ya kaurace wa taba sunan Allah koda da wane harshe aka rubuta shi. Mas’ala ta 235:Idan mutum ya yi alwalla ko wanka kafin lokacin salla, sannan kuma wankan ko awallar sun inganta kuma ya yi su ne da niyyar kusanci ga Allah ya wadatar ya yi salla da su. Mas’ala ta 326: mustahabbi ne mutum ya yi alwalla don yin sallar gawa ko ziyarar makabarta ko harammin ma’asumai a.s.haka nan idam mutum yana so ya kasance tare da kur’ani. Ko ya karanta shi ko ya rubuta shi,Haka nan mustahabbi ne mutum ya yi alwalla don shafar gefen rubutun kur’ani ko lokacin barci.Haka nan mustahabbi ne mutum ya yi alwalla don jaddadawa wato dama yana da alwalla sai ya kara yi.idan mutum ya yi alwalla don wadannan abubuwan da muka fada a baya yana iya yin kowane aiki da wannan alwallar ba sai ya sake yin alwalla ba don yin wani aikin da yake bukatar alwalla.misali ya yi alwalla don ya karanta kur’ani yana iya yin salla da wannan alwalla. Abubuwan da suke bata alwalla: Mas’ala ta 327:Abubuwa bakwai n eke bata alwalla: 1-Kashi 2-fitsari. 3-tusa 4-barci mai nauyi ta yadda mutum ba ya ji kuma ba ya ganin abin da yake faruwa. 5-Abin da ke gusar da hankali. 6-istihadha anan gaba zamu yi bayaninta. 7-Dukkan abin ke wajabta wanka, kamat janaba da makamantanta.Taba gawa yana shiga cikin wannan hukuncin akan ihtiyati.
|