Hukunce-Hukuncen wanka:
Mas'ala ta 372: A wajen wankan irtimasi dole ne jikin mutum ya kasance
mai tsarki, amma wankan tartibi ba dole ban e dukkan jikin mutum ya kasance mai
tsarki,Idan dukkan jikin mutum ya ka sance mai najasa, yana iya wanke bangaren
dayake so ya wanke wato idan zai wanke bangaren dama sai ya wanke shi sannan
haka nan bangaren hagu, ba sai ya tsabtace dukkan jikinsa ba kafin ya fara
wankan sabanin wankan irtimasi dole sai ya tsabtace dukkan jikinsa kafin ya fara
wankan.
Mas'ala ta 373:zufar janabar haram ba najasa ba ce, don haka idan
mutumu ya samu janaba ta haram idan ya yi wanka da ruwan zafi wankannsa ya
inganata.
Mas'ala ta 374:Idan ya kasance yayin wankan wani wuri ya rage baa
wanke ba, daga cikin jiki wanda koda girmansa kwatankwacinsa gashin
kai yake, wanka ya baci.
Amma ba dole ba ne wanke wuraren da ba a gani daga cikin jiki kamar cikin
hanci da kunne.
Mas'ala ta 375:Idan mutum yana shakka akan cewa shin wannan wurin yana
daga cikin zahirin jiki ko yana daga cikin wuraren da ba a gain, anan ihtiyat
wajib a wanke wajen,sai idan a da ya ksance daga cikin wuraren da ba a gani, sai
yanzu murtum yana shakka akan cewa shin yana daga ciin wuraren da ake gani ko
kuwa, anan wanke shi ba wajibi ba ne.Mas'ala ta 376:Idan kofar da ake sanya dan
kunne ta kasance babba yadda za'a iya ganin cikinta anan dole ne a wanke
cikinta.Amma idan ba a ganin cikinta ba dole ba ne a wanke cikinta.
Mas'ala ta 377:Dole ne a gusar da abin da zai iya hana ruwa taba
fatar mutum, idan mutum bai samu yakini ba akan cewa ya gusar da abin zai iya
hana ruwa taba fatarsa, sai ya yi wanka, wankansa bai wadatar ba.
Mas'ala ta 378:Idan lokacin da mutum yake cikin wanka sai ya yi shakka
akan cewa shin abin da zai iya hana ruwa isa bisa fatarsa yana nan ko kuwa
ya gushe,idan ya zamana wannan shakkar tasa zata iya zama abin kula ga masu
hankali, anan dole ne ya bincika don ya tabbatar da cewa ya gusar da abin,
sannan ya cigaba da wabkansa.
Mas'ala ta 379:Dole a wajen wanka mutum ya wanke gashinsa gajere wanda
ake iya lissafa shi daga jikin jikin mutum,amma ihtiyat wanke a wanke shima
dogon gashi.
Mas'ala ta 380:Dukkan sharuddan da aka fada wajen ingancin alwalla,
kamar kasancewar ruwa mai tsarki,nah alas a wajen ingancin wanka ma shradi ne su
kasance haka.Amma ba dole ban e a wajen wanka a wanko daga sama zuwa kasa, idan
mutum ya wanko daga kasa zuwa sama wankansa ya inganta sabanin alwalla,Hakan a
wajn wankan tartibi ba dole ba ne mutum bayan gama wanke bangaren dama ya cigaba
da wanke bangaren hagu ba tare da bata lokaci ba kamar a cikin alwalla, a cikin
wankan tartibi mutum yana iya wanke wani bangare sai ya bari sai wani lokaci
sannan ya dawo ya cigaba, misali mutm yana iya wnake kansa sai ya bari sai bayan
wani lokaci sannan ya dawo ya wanke bangaren dama, sai mace mai istihala wadda
anan gaba zamu fadi hukuce-hukunceta.
Mas'ala ta 381:Wanda ya yi nufin ba zai bad a kudi ba a gidan wanka ko
kuma yana nufin ya yi ba shi,amma bai gaya wa mai gidan wankan ba,yana so sai y
agama sannan ya gamsar da shi cewa zai ba shi daga baya, anan wankansa ya ba ci
koda ya gamsar da shi bayan ya gama wankan.
Mas'ala ta 382:Idan mutum yana so ya biya kudin gidan wanka da kudin
haram ko kuma kudin dab a a fitar musu da zakka ba, anan wankasa ya baci.
Mas'ala ta 383:Idan mai gidan wanka ya amice kudin wankan su zama
bashi, amma sai yaksance mutum ya yi nufin ya hana kudin ko kukma yana nufin ya
biya da kudin haram, anan wankansa ya baci.
Mas'ala ta 384:Idan mutum ya tsarkake wajen fitar kashi da ruwan da
yake ajiye a gidan wanka kafin mutum ya yi wankan,sai mutum ya yi shakka akan
cewa shin tunda yayi tsarki da wannan rowan shin mai gidan wanka ya aiminta day
a yi wankan ko kuwa bai aminta ba,anan wankansa ya baci, sai dai idan ya gamsar
da shi kafin ya fara wankan.
Mas'la ta 385:Idan mutum ya yi shakka akan cewa shin ya yi wankan ko
kuwa bai yi ba,anan dole ne ya yi wanka,amma idan bayan ya gama wanka sai ya yi
shakka akan cewa shin wankasa ya inganta ko kuwa bai inganta ba, anan ba sai ya
sake wanka ba wankansa ya wadatar.
Mas'ala ta 386:Idan mutum yayin da yake cikin wanka sai ya yi wani abu
wanda yake bata alwalla kamar tusa ko fitsari, yana iya cigaba da wankansa bayan
ya gama sai ya yi alwalla,duk da yake ihtiyat shi ne ida wankan sannan ya
sake wankan da ma'anar rama abin da ke kansa, amma alwalla a wannan halin wajibi
ce bayan ya gama wankan.
Mas'ala ta 387:Idan mu8tu yana ganin cewa lokaci zai isa ya yi wanka
sannan ya yi salla, amma bayan y agama wankan sai ya fahimci cewa a she lokacin
kawai zai isa ya yi wanka, anan wankansa ya inganta.
Mas'ala ta 388:Wanda ya samu janaba, amam sai ya yi shakka akan cewa
shin ya yi wanka ko kuwa bai yi ba, anan sallolin day a yi kafin wannan shakkun
sun inganta amma dole ne ya yi wanka saboda sallolin gaba.
Mas'ala ta 389:Wanda yake da wankan wajibi da yawa akansa, yan iya yin
niyya gaba daya ya yiwankan guda ya wadatar, ko kuma ya yi waken daban-daban.
Mas'ala ta 390:Idan ya ksance akwai rubutun ayar kur'ani akan jikin
mutum dole ne mutum ya goge wannan rubutun kafin ya yi janaba, idan kuwa ba haka
ba idan ya riga ya yi janaba dole ne ya yi wanka cikin sauri. Sanan dole ne ya
kula kada ya taba wajen rubutun da hannunsa yayin wankan, sai dai kawai ya zuba
ruwa a wajen ta yadda ruwan zai yi gudu a kai.
Mas'ala ta 391:Wanda ya yi wankan janaba ba dole ban e ya yi alwalla
don yin salla,haka nan idan mutum ya aiwatar da wani daya daga cikin wankan
wajibi yana iya yin salla da shi, amma banda wankan mai istihala matsakaiciya,
duk da yake idan ba wankan janaba ba ne ya kamata ya yi alwalla sannan ya yi
salla.
|