|
||||||||||||||||||||||
|
Wankan tartibi:Mas'ala ta 361: Abin da ake nufi da wankan tartibi shi ne, mutum ya yi niyyar wanka sai ya fara wanke kansa da wuyansa, sannan sai ya wanke bangaren jikinsa na dama sannan ya wanke bagaren hagu.Idan da mutum sakamakon mantuwa ko rashin sani sai ya yi sabanin yadda muka fada, wankasa ya baci. Mas'ala ta 362:Za a wanke rabin cibiya da rabin al'ura tare da rabin jiki, duk da cewa a wanke su duka tare da rabin jikin ya fi, wato sau biyu kenan ya yin wanke bangaren dama da kuma yayin wanke hagu. Mas'ala ta 363:Don mutum ya samu yakini cewa ya wanke duk bangarorin guda uku,wato kai bangaren dama da hagu, ya kamata yayin wanke kowa ne bangare ya hada da bangaren da ya riga ya wanke domin ya sami yakini.Kai ihtiyat mustahab shi ne mutum ya wanke rabin wuyansa na dama tare da rabin jikinsa na dama haka nan na hagun. Mas'ala ta 364: Idan bayan mutum ya gama wanka, sai ya samu yakini akan cewa lallai akwai inda bai wanke ba cikin jikinsa, sannan kuma bai san ina ne bai wanke ba, anan sai ya sake wankan daga farko. Mas'ala ta 365:Idan mutum bayan ya gama wanka sai ya gane cewa bai wanke wani bangare ba, misali sai ya kasance bangaren hagu ne, anan idan ya wanke wannan bangaren kawai ya wadatar.Amma idan bangaren dama ne bayan ya wanke dammar dole ne ya sake wanke hagun, haka nan idan wani wuri ne daga cikin kai ko wuya ke bai wanke ba, anan bayan ya wanke wurin sai ya sake wanke duka bangaren hagu da na dama baki daya. Mas'ala ta 366:Idan kafin mutum ya gama wanka sai ya yi shakka akan wanke wani bangare na sashen hagu, idan ya wanke wannan wurin kawai ya wadatar. Amma idan ya kasance kafin ya fara wanke sashen hagu sai ya yi shakka a kan shin ya wanke wani bangare na dama ko bai wanke ba, ko kuwa kafin ya fara wanke sashen dammar sai ya yi shakka akan wanke wani bangare daga cikin kai ko wuya, anan ba dole ba ne ya kula da wannan shakka ta sa. Wankan irtimasi: MAs'ala ta 367:dole a wankan irtimasi mutum ya saka dukkan jikinsa a cikin ruwa a lokaci guda, saboda haka idan mutum ya yi niyyar wanka si ya shigar da baki dayan jikinsa a cikin ruwa, ta hanyar tsundumawa a lokaci guda ko kuwa a hankali ya shigar da jikin nasa, wankansa ya inganta. Mas'ala ta 3678:A lkacin wankan irtimasi idan jikij mutum ya kasance a jikin ruwa sannan sai ya yi niyyar wanka sai motsa jikinsa a cikin ruwan wankansa ya inganta. Amma dai ihtiyat mustahab shi ne mutum ya yi niyyar wanka kafin ya shiga cikin ruwan. Mas'ala ta 369:Idan mutum bayan y agama wankan irtimasi sai ya gane cewa akwai wani wuri daga cikin jikinsa wanda ruwa bai taba ba, anan sai ya sake wankan daga farko. Mas'ala ta 370:Idan mutum ya kasance ba shi da damar yin wankan tartibi amma yana da dammar yin wankan irtimasi, anan dole ne ya yi wankan irtimasin. Mas'ala ta371:Wanda ya dauki azumin wajibi ko ya yi haramin umura ko hajji ba zai iya yi n wankan irtimasi ba,amma idan a bisa mantuwa ya yi wankan irtimasi ya inganta.
|