Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Hukunci kashi da fitsari:

Mas'ala ta 61:wajibi ne mutum yayin da zai biya bukatarsa ya rufe al'aurarsa daga sauran mutane wadan da suke baligai ne. Koda kuwa mahaifiyarsa da kanwarsa ne ko kane. Sannan mahaukaci ko karamin yaro idan suna gane abu suma wajibi ne a sirranta al'aurarsa gabansu. Amma tsakanin miji da mata ba  laifi suna iya ganin al'aurar junansu.

Mas'ala ta 62:Ba dole ba ne mutum ya rufe al'aurarsa da wani tufafi na musamman ko da da hannu ne ya wadatar.

Mas'ala ta 63:dole ne mutum yayin kashi ko fitsari ya kauce wa alkibla ko ba ta baya.

Mas'ala ta 64:idan ya kasance ya yin fitsari ko kashi mutum ya kalli alkibal ko ya ba ta baya , amma ya kautar da al'aurarsa daga alkibla to bai isar ba,sannan idan ya kasance b aya kallon kibla to mafi dacewa shi ne ya kauracewa juya al'aurarsa zuwa kibla.

Mas'ala ta 65:Yayin wanke wurin fitsari ko kashi ba kaifi mutum ya kalli kibla ko ya bata baya.amma mustahabbi ne ko a cikin wannan halin ya kauce ma yin hakan.

Mas'ala ta 66:Idan ya kasance mutum ya zama dole ya juya zuwa libla don kaucewa daga wadnsu kada su ga al'aurarsa ko sakamakon wani dalili da ya zana wajibi ya kauce zuwa kibla babu laifi.

Mas'ala ta 67:,ya fi dacewa  yaro ya kauce wa  kibla yayin kashi ko fitsari, Amma idan shi da kanshi ya zauna ba dole ba ne a canza shi.

Mas'ala ta 68:Yin kashi ko fitsariya haramta a wurare guda hudu:

1-A lungu da baya fita, sai da izinin masu gidaje wajen.

2-A cikin fili ko kangon gida idan mai shi bai bad a izini ba.

3-A wuraren da suke na wasu ne na musamman kamar wata makaranta.

4-makabartar musulmi idan ya kasance rashin girmamamwa ne garesu.

Mas'ala ta 69:Ba a tsarkake  wurin fitsari da abin da ba ruwa ba, idan aka gusar da fitsari ana iya tsarkake wurin da ruwa sau daya ya wadatar,duk da cewa mafi dacewa a yi sau biyu.Amma wadanda suke yin fitsari in dab a wurin da aka saba ba sakamkon wata matsala, dole ne a  wanke sau biyu.

Mas'ala ta 70: Idan aka tsarkake wurin kashi da abin d ruwa ba, to dole ne a tabbatar da cewa ya fita babu sauran shi.Amma don wari ko launi sun rage babu wani laifi.Idan aka wanke kashi wankewar farko ya zama bau sauran kashin ba dole ban e sai an kara.

Mas'ala ta 71:Idan aka tsarkake wurin kashi da dute ko wani makamancinsa duk da yake akwai matsala wajen tsarkin amma yin salla da shi ba matsala.

Mas'ala ta 72:Ba dole ba ne a goge wurin kashin da dutse guda uku ko takarda guda uku,ya isar a tsarkake wurin da dutse ko takarda guda daya, amma ya zama na an goga a kalla sau uku,amma idan aka gogen wurin da kashi ko wani abu dai day a kamata a girmama shi, kamar takardar da akwai sunana Allah a kai, mutum ba zai iya yin salla bad a wannan tsarkin.

Mas'ala ta 73:A wurare uku kawai da ruwa ake iya tsarkake wurin kashi:

Na daya:Idan tare da kashin wata najasa ta fito, kamar jini.

Na biyu:Idan najasar daga waje ta samun wajen kashin.

Na uku:Idan wurin kashin ya samu najasa fiye da yadda aka saba.

Ban da wadan nan wuraren ana iya tsarkake wurin kashin da ruwa ko da dutse da takarda kamar yadda zamu fada a nan gaba, duk da cewa wankewa da ruwa ya fi.

Mas'ala ta 74:Idan mutum ya yi shakka akan cewa shin ya yi tsarki ko bai yi ba,ko da ya kasance koda yaushe bayan ya gamakashi ko fitsari yana yin tsarki, abin da ya fi shi ne, ya sake yi domin ya samu yakini.

Mas'ala ta 75:Idan mutum  bayan ya yi salla sai ya yi skakka akan shin ya tsarki ko bai yi ba, sallar day a yi ta inganta ,amma dole ya yi tsarki don sallolin da zai yin an gaba.

Istibra'i:

Mas'ala ta 76:Istibra'i  wani aiki ne mustahabbi da maza ke yi bayan sun gama fitsari,Wannan aiki kuwa yana da kashe -kashe,amma wanda duk ya fi su muhimmanci shi ne,wanda ake yi bayan an gama fitsari, Idan wurin da kashi yake fita ya samu najasa yayin fitsari, sai a wanke wajen da farko, sannan sai a sa hannun hagu daga kusa  da in da  kashi yake fita a matso zuwa farkon al'aura sau uku, sai a sa babban yatsa bisa al'aura a sanya yatsa na tsakiya a karkashi a matse zuwa kan al'aurar sau uku.sanan sai a kama kan ala'urar a matsae sau uku.

Mas'ala ta 77:Ruwan da yake fita yayin da mutum yake wasa da matarsa ana kiransa maziyyi, sannan kuma mai tsarki ne.Sannan ruwan da yake fita bayan maniyyi ana kiransa waziyyi sannn mai tsarki ne.Ammam ruwan da yake fitowa wata sa;a bayan fitsari ana kiransa wadiyyi, kuma mai tsarki ne.saboda haka idan mutum bayan ya yi fitsari sannan ya yi Istibra'i kamar yadda muka fada a sama, idan wani ruwa ya fito bayan nan, sai mutum ya yi shakku akan cewa fitsari ne ko kuwa daya daga cikin abubuwan da muka fada, hukuncinsa mai tsarki ne.

Mas'ala ta 78: Idan mutum ya yi shakku akan cewa ya yi istibra'i ko kuwa bai yi ba, sannan sai wata lema ta fito daga gare shi, sannan yana shakkun cewa shin mai tsarki ce ko kuwa? Hukuncinta  najasa ne, domin ba da  ya tabbas akan ya yi istibra'i.Saboda haka idan ya riga ya yi al'walla ta ba ci, amma idan yana shakku akan cewa shin istiba'in da ya yi shin ya yi dai- dai ko bai yi dai-dai ba, idan ya ji wata lema hukuncinta  mai tsarki ce sannan idan ya yi alwalla ta inganta.

Mas'ala ta 79:Idan mutum bai yi istibra'i ba sannan tsawon lokacin ya  wuce kuma ya samu yakini akan cewa fitsari bai rage ba a cikin al'aurarsa,, sai ya ji wata lema ta fito daga gare shi , hukuncin wannan lema mai tsarki ce. Sannan  alwallarsa ba ta ba ci ba.

Mas'ala ta 80: Idan mutum bayan ya yi istibra'i sai ya yi alwalla, sannan sai ya ji wata lema, sai ya yi tunanin cewa shin fitsari ne ko maniyyi? Wajibi ne ya yi wanka sannan ya yi alwalla don yin ayyukan ibada.Amma idan dama  ya kasance bai yi alwalla ba to idan ya yi alwalla kawai ta  wadatar.

Mas'ala ta 81:Mace ba ta yin istibra'i don haka idan ta ji wata lema sai ta  yi shakku akan cewwa shin mai tsarki ce ko najasa, hukuncinnta mai tsarki ce, sannan ba ta bata wanka ko alwalla.

Mustahabbai da makaruhai wajen kashi da fitsari:

Mas'ala ta 82:Mustahabbi ne mutum ya yi kashi ko fitsari a wurin da ba wanda yake ganinsa,Sannan idan zai shiga bayi mustahabbi ne ya shiga da kafar hagu sannan ya fito  da kafar dama. Sannan mustahabbi ne mutum ya rufe kansa yayin da yake kashi ko fitsari,sannan ya ba bangaren kafar hagunsa nauyi.

Mas'ala ta 83:fuskantar rana ko wata yayin kashi ko fitsari makaruhi ne, Amma idan mutum ya rufe al'aurarsa ba laifi kuma ba makaruhine ba.Sannan makaruhi ne mutum ya kalli wajen da iska yake bugawa yayin kashi ko fitsari, sannan haka nan a bisa hanya ko titi,sannan makaruhi ne a cikin lungu ko kofar gida  ko karkashin itaciyar da take yin 'ya'ya.Sannan makaruhi ne cin wani abu yayin kashin ko fitsari ko kuma dadewa a wajen,sannan makaruhi ne yin tsarki da hannun dama.sannan haka nan yin magana yayin kashi ko fitsari makruhi ne idan dai ba ya zama dole ba.Haka babu laifi mutum ya ambaci sunan Allah.

Mas'ala ta 84: Makaruhi ne yin fitsari daga tsaye ko kuma yin fitsari bisa kasa mai tauri(hako)ko kuma akan ramin dabbobi da kwari, haka nan yin fitsari a cikin ruwa, musamman ruwan da baya gudu.

Mas'ala ta 85: mutum ya ki yin kashi  ko fitsari alhali yana jinsa makaruhi ne, idan har zai cutar ma dole ne ya kauce ma kin yinsa.

Mas'ala ta 86:Mustahabbi ne mutum kafin ya yi salla ya yi fitsari ko kafin barci, sannan mustahabbi ne mutum ya yi fitsari kafin ya yi jima'i ko bayan ya yi jima'i, bayan ya fitar da  maniyyi.

Baya kanu Gaba