Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Najasa

Mas'ala ta 87:Abubuwan da ke  najasa guda goma sha daya ne,sune kamar haka:1fitsari 2 kashi 3 maniyyi 4mushe 5 jini 6 kare 7 alade 8 mushiriki 9 giya 10  tsumin da ke sa maye. 11zufar rakumin da ke cin najasa.

1/2:Fitsari da kshi:

Mas'ala ta 88 kashi da fitsarin mutum najasa ne haka na dabbobin da cin  naman namansu haram ne, sannan jininsu mai tsartuwa ne, wato idan da za'a yanka su jininsu zai yi tsartuwa.

Mas'ala ta 89:Kashi da fitsarin tsuntsayen da cin anmansu haram ne, mai tsarki ne.

Mas'ala ta 90:fitsari da kashin dabbobin da ke cin najasa, najasa ne.haka ma kashi da fitsarin dabbar da mutum ya sadu da ita najasa ne.haka nan ma naman  tunkiyar da ta sha nonon alade ta girma.

3-Maniyyi:

Mas'ala ta 91:Maniyyin dabbar da ke  da jinin mai tartuwa najasa ne.

4-Mushe

Mas'ala ta 92:Mushen dabbar da ke da jini mai tsartuwa najasa ne,da kanta ta mutu ko kuwa anyanka ta ne ba ta hanyar da shari;a ta yarda ba.Amma kifi tun da ba ya da jini mai tsartuwa ko da ya  mutu cikin ruwa ba najasa ba ne.

Mas'ala ta 93:Sassan jikin dabba mushe kamar gashi, kashi da hakora, wato wadan da ba su da rai, idan na dabbar da ba kare ba ko alade ne masu tsarki ne.

Mas'ala ta 94:Idan aka ciri wani bangare na jikin mutum ko dabbar da ke da jini mai mai tsartuwa a lokacin da suke da rai, sannan daga bangaren da yake da jini, shi ma najasa ne.

Mas'la ta 95:Wata fata ta  jikin mutum idan dama ta kusa faduwa ta yadda ba ta da rai,sa mutum ya ida cire ta, ba najasa ba ce.

Mas'la ta 96:Kwai wanda ya fado daga kaza matatta koda fatarsa ba ta ti kwari ba, mai tsarki ne.

Mas'la ta 97:Idan akuya ta mutu nonon da ke cikin hantsarta mai tsarki ne, amma dole ne a zuba wa bayan hantsar ruwa.

Mas'ala ta 98:Abubuwan da ake kawao daga kasashen da ba na musulmi ba, kamar sabulu,mai, turare da makamantansu, Idan mutum ba ya da yakini akan kasancewarsu najasa, masu tsarki ne.

Mas'la ta 99:Nama, fata da kitsen da yake hannun musulmi, mai tsarki ne. Amma Idan mutum ya san cewa wancan musulmi ya sami wannan naman ne daga hannun kafiri, sannan bai yi bincike ba kana cewa shin mai tsarki ne ko kuwa,Banajsa  ba ne amma cinsa yana da matsala haramun ne.Sannan salla da fatar wannan dabbar ba ta inganta.

5-Jini

Mas'ala ta 100:Jinin mutum da duk dabbar da ke da jini mai tsartuwa najasa ne,saboda haka jinin kifi tun da ba shi jini mai tsartuwa ba najsa ba ne.

Mas'ala ta 101:Idan aka yanka dabba kamar yadda shari'a ta bayyana, kuma jiniya gama zuba kamar yadda aka saba, amma sai wani yage cikin naman, wannan wanda ya rage ba najasa ba ne.Amma idan wannan jini sakamakon nimfashin da dabbar ta yi ne yayin yanka sai ya koma cikin ciki, ko kuma sakamakon an aza wuyanta wani wuri mai tudu ne sai ya koma ciki, to wannan najasa ne.

Mas'ala ta 102:Jinin da yake cikin kwai mai tsarki ne amma abin da yafi a kaurace ma sa.

Mas'ala ta 103: mai launi ruwan dorowa da ke cikin kwai idan bai gauraya ba jini  mai tsarki ne.

Mas'la ta 104:Jinin da kae ganin yayin shan madara najasa ne kuma madarar ma najasa ce.

Mas'ala ta 105:Jinin da yake fitowa jikijn dasashi idan ya gauraya da yawu ta yadda ya bace a cikin yawu ba a ganinsa, mai tsarki ne.saboda haka hadiye  wannan yawun babu laifi.

Mas'ala ta 106:jinin da yake mutuwa karkashin farce sakamakon bigewa da mutum ya yi ta yadda ba za,a ce masa jini ba, to wannan jinin da ya mutu mai tsarki ne.Amma idan ana iya  ce masa jini yana zama najasa idan kawai farcen ya fashe jinin ya fito daga ciki. Saboda haka anan idan ba zai zama wahala ba dole ne a wanke yayin alwalla ko wanka, amma idan ya kasance zai zama wahala to ana iya wanke gefe ta yadda za a rage najasar, sai a samu wani kyalle a jika shi da ruwa a dora bisa wuri sai shafa a sama yayin alwalla.

Mas'ala ta 107:Idan mutum bai san da cewa ba jini ya mutu karkashin fatarsa sakamkon bigewa da ya yi sai ya fito waje, ba najasa  ba ne.

Mas'ala ta 108:Idan jini ya fada ckin tukunya yayin dahuwar abinci, dukkan abincin da tukunyar sun zama najasa,tafasa da zafin wuta ba ya tsarkake su.

6/7-Kare da alade

Mas;ala ta 109:Kare da aladen da ke rayuwa bisa doron kasa, hatta gashi, kashi da gashinsu, har lemar jikinsu najasa ce.Amma kare da laden ruwa ba najasa ba ne.

8-Mushiriki

Mas'la ta 110:Abin da ake nufi da mushiruki shi ne wanda yake bauta wa wani abu wanda ba Allah ba. Ko kuma yana bauta wani tare da Allah.Idan mutum ya kasance haka najasa ne.Amma wadan da suka yi imani da cewa Allah daya ne,Sannan sun yarda da wani daga cikin annabawan Allah, kamar yahudawa da kiristoci da majus, wadannan ba najasa ba ne.kuma su ne ake ce wa Ahlul kitab.Amma idan suka zama mushirikai sakamakon canza addininsu, suma hukuncinsu zai zama kamar sauran mushirikai.Sannan wadan da ba su da addini suma hukncin daya da mushirikai najasa ne. Sanna makiya ahlul bait a.s. (Nasibi) suma najasa ne,Haka ma khawarij da sauran musulmin da suka zama kushirikai kamar wadan da suke bauta wa Imam ali a.s. ko wadan da suka yi inkarin daya daga cikin wajiban addini ta yadda inkarinsu zai koam ga inkarin Ubangiji da manzo s.a.w.a, suma najasa ne.

Mas'ala ta 111:Dukkan jikin mushiriki lemar jikinsa  har da gashinsa najasa ne.

Mas'ala ta 112:Idan ua da uban kakannin yaron da  bai balaga ba  suka kasance mushirikai shima wannan yaron najasa ne.Amma idan daya daga cikinsu ya musulunta shi ma yaron zai zama mai tsarki.

Mas'al ta 113: Wanda ba 'a san cewa musulmi ne ba ko  a'a ,sannan a da  ma ba a san cewa ko shi musulmi ne  ba ko kafiri, sai a yi ma sa hukuncin mai tsarki.Amma ba y a da sauran hukuncin musulmi.Misali ba zai iya auran  mace musulma ba,ko kuma a rufe a makabartar musulmi.

Mas'ala ta 114:Idan musulmi ya zagi daya daga cikin ma'asumai goma sha hudu ko ya yi adawa da daya daga cinsu, to shi najasa ne.

Mas'ala ta 15:Ahalul kitabi(yahudawa da kiristoci) ba najasa ba ne:

Mas'ala ta 116:Murtad wanda ya bar musulunci, kasancewarsa najasa ko mai tsarki ya danganta da kungiyar da ya shiga bayan ya bar musulunci, wato idan ya shiga cikin kungiyar da su najasa ne, to sai a yi masa hukunci da najasa,amma idan ya shiga cikin kungiyar da ba najasa babne kamar yahudawa da kiristoci to shima ba najasa ba ne.

9-Giya

Mas'ala ta 117:Giya da duk abin  ya ke sa mutum maye,Idan ya kasance mai ruwa najasa ne,Amma kamar wi-wi wato wanda ba ruwa ba ne koda ruwa ya shiga cikinta ba najasa ba ce.

Mas'ala ta 118:Alkol fari wanda ake magani da shi wanda ba ya da gauraye, likitoci ke amafani da shi mai tsarki ne. Sai dai idan an same shi ne daga giya ko makamancinta abin da ke sa maye, idan ya kasance haka najqsa ne.Haka sauran acid wanda ake amfani da shi a asibitoci shima mai tsarki ne, Haka nan alkahol din da  ake amfani da shi wajen masana'antu kamar wanda ake sawa cikin turare maitsarki ne. Saboda haka turaren da aka hada da alkahol  shima mai tsarki ne.

Mas'ala ta 119: Idan aka tafasa inabi shansa haramun ne amma ba najasa ba ne.

Mas'ala ta 120:Amma idan aka tafasa dabino shima mai tsarki ne kuma shan sa ba ya da laifi.

10-Tsumi mai sa maye

Mas'ala ta 121:Tsumin da aka yi sa daga acca najasa ne, amma wanda likita ya ba da umurni aka yi daga acca din don magani, wanda ake kira(ma'ussha'ir) mai tsarki ne.

11-Zufar rakumin  da yake cin najasa

Mas'ala ta 122:zufar rakumin da yake cin najasa, najasa ce.Amma idan dabbobi daban ba rakumi ba suke cin najasa, zufarsu ba najasa ba ce.

Zufar janabar haram

Mas'ala ta 123: zufar janabar haram ba najasa b ace,Amma abin da  ya fi shi ne a kaurace wa jiki da tufafin da aka yi janabr da su, wajen yin salla.

Mas'ala ta 124:Idan ya kasance a lokacin da, saduwa da mace haram ne kamar cikin watan azumi da rana,idan mutum ya sadu da matarsa a lokacin, abin da  ya fi shi ne ya kaurace wa yin salla da jiki da  tufafin da ya yi janabar.

Mas'ala ta 125:Idan wanda ya yi janaba ta haram ya kasa yin wanka,sai ya yi taimama maimakon wanka, to abin da ya fi shi ne ya kauracewa salla da tufafi da zufar  jikinsa da ya yi wannan janabar.

Mas'ala ta 126:Idan mutum ya yi janaba da haram sai kuma ya sadu da matarsa, abin  da ya fi shi ne ya kauce wa yin salla da zufar jikinsa da tufafinsa.Amma idan ya fara yin janaba ne da matarsa,sannan sai ya yi janabar haram, ba dole ba ne ya kauce wa yin salla da wannan zufar.

Baya kanu Gaba