Hanyar tabbatar da najasa:
Mas'ala ta ta 127:Ana tabbatar da najasar abut a hanyoyi
guda uku kamar haka:
Hanya ta daya:Mutum ya sami yakini akan cewa abu mai najasa ne.Amma idan mutum
yana zoton kasancewar abu najasa ne, ba dole ban e ya kaurace wa wannan abin.Sai
dai idan mutum yaza zato net a yadda mutane sukan lisafa wannan zaton yakini, to
anan ma ba za a yi abin hukunci da najasa ba.Saboda haka cin abinci ko shayi a
irni wuraren ann da kowa yake zuwa hard a muta nen da bas u kulawa da
najasa,idan dai mutum ba ya samu yakini ba akan cewa abi yana da najasa to zai
masa hukunci ne da mai tsarki ne.
Hanya ta biyu:ko wanda yake da abu y ace wannan abin najasa ne, ko kuma wanda ke
kula da abu ya fadi cewa wannan abin yana da najasa, kamar matar mutum ko
yaronsa ya fadi cewa abu yana da najasa,a wannan halin abu yana kasancewa mai
najasa.
Hanya ta uku:Mutane adalai guda biyu su fadi cewa wannan abin najsa ne,amma idan
adali guda daya ya fadi cewa wannan abin najasa ne abin da ya fi shi ma an
kaurace wa abin.
Mas'ala ta ta a28:Idan mutum bai san abu mai najasa ko marar najasa
ba, misali bai san cewa zufar rakumi mai cin najasa, najasa ce ko ba najasa ce
ba, anan dole ne mutum ya yi tambaya don ya san hukuncin abu,Amma idan ya san
hukunci amma yana shakku akan najasar abu, to hukunci abin mai tsarki ne.
misali idan yana shakku akan kasancewar wannan jinin shin na mutum ne kona
sauro, anan sai hukunci da tsarkinsa.
Mas'la ta 129:Idan mutum yana shakku akan abin da yake najasa cewa yanzu ya
zama mai tsarki ko kuwa yana nan yadda yake,to zai yi masa hukunci da mai najasa
ne.Amma idan mutum yana shakku akan abin da yake mai tsarki ne amma yanzu shin
ya zama mai najasa ko kuwa to zao masa hukunci da mai tsarki.
Mas'ala ta ta 130:Idan mutum ya san cewa daya daga cikin tufafinsa ko
kwanonin da yake amfani da su ya zma mai najasa, amma bai san wane ne daga ciki
bay a zama mai najasar, dole ya kaurace wa dukkan biyun,Haka nan ma idan
yana shakku cewa shin wannan tufafin da yake amfani da shi ne ya zama mai najasa
ko kuwa wanda ba ya amfani da shi ne na wani ne, annan ma dole ya kaurace nasa
wanda yake mafani da shi.
Hanyar da abu mai tsarki yake zama mai najasa:
Mas'ala ta ta 131:Idan abu mai tsarki ya hadu da abu mai najasa kuma
daya daga cikinsu ko kuma duka biyun sun kasance masu lema ne, kuma lemar daya
ta shafi dayan, to mai tsarki ya zama mai najasa.Amma idan ya kasance lemar daya
ba ta isa zuwa ga dayan ba to, mai tsarkin bai zama mai najasa ba.
Mas'ala ta ta 132:Idan abubuwa guda biyu daya mai najasa daya kuma mai
ysarki suka hadu, amma sai mutum ya yi shakka akan cewa shin daya daga cikinsu
ya ksance mai lema ko kuwa, anan mai tsarkin bay a zama najasa.
Mas'ala ta ta 133:Idan mutum bai san cikin abubuwa guda biyu ba wane
ne mai najasa sai wani abu mai lema ya taba daya daga cikinsu, to wannan abun
mai lema ba ya zama najasa.
Mas'ala ta ta 134: Kasa ko tufafi da makamancinsa idan sun kasance
masu lema, duk bangren da najasa ta taba daga cikinsu zai zama najasa,Amma
sauran bangarorinsu zasu kasance masu tsarki kamar da,haka nan ma irinsu kankana
da makamantansu kawai bangaren da ya taba najasa yake zma mai najasa.
Mas'aal ta 135:Idan madara ko mai sun kasance masu ruwa, idan wani
bangare daga ciki ya samu najasa dukkansu sun zama najasa.Ammam idan sun kasance
a daskare to kawai inda najasa ta tab aya zama mai najasa.
Mas'ala ta ta 136:Idan kuda ko makamancin ya sauka abu mai
najasa, sananna suka zauka akan abu mai lema, idan mutum ya tabbatar da cewa
akwai najasa jikinsu; to abin da suka zauna akai mai lema zai zama mai najasa;
amma idan ba su da tabbas akan cewa kwai najasa a jikinsu to, abin yanan nan mai
tsarkinsa.
Mas'ala ta ta 137:Idan jikin mutum ya kasance mai ufa sannan inda yake
da zufar ya samu najasa to duk inda zufar ta kwarara ya zama mai najasa, amma
idan zufar ba kwarara zuwa ko'ina ba to kawai inda ya samu najasar ne ke da
najasa, sauran bangarorin jikin kuwa mai tsarki ne.
Mas'ala ta ta 138: Abin da ke fitow a daga hanci ko makogaro idan ya
kasance yana da jini wurin da ya samu jinin zai zama mai najasa.,amma sauran
wurin da bai samu ba yana nan mai tsarkinsa kamar da.
Mas'la ta 139: idan buta ta kasance mai kofa daga kasa wato ta yadda
ruwa yana zuba daga kasa,idan aka ajiye ta bisa kasa mai najasa ta
yadda wannan ruwan da yake zuba kas aya hadu da ruwan da yake cikin butar, to
shima ruwan da yake cikin butar zai zama mai najasa, amma idan ruwan butar bai
hadu da ruwan da yake bisa kasa mai najasa ba to , na butar ma b aya zama mai
najasa.
Mas'ala ta ta 140:Idan wani abu ya shiga cikin jikin mutum ta yadda ya
hadu najasa, amma lokacin da aka fito da abin babu najasa jikinsa, mai tsarki
ne.saboda haka idan aka yi wa mutum allura kuma ta yadda ta hadu da jini yayin
da ka fito da ita babu jini tare da iata ba ta zama mai najasa.Haka ma idan yawu
ko majina ta hadu da jini a cikin hanci ko baki amma yayin da suka fiti a waje
babu wannan jinin masu tsarki ne.
|