Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Hukuncin najasa:

Mas'ala ta 141:Sanya najasa bisa rubutun kur'ani ko ko takaradarsa haramun ne, Idan kur'ani ya samu najasa dole a yi sauri a tsarkake shi.

Mas'ala ta 141:Idan bangon kur'ani ya samu najasa dole a wanke shi.

Mas'ala ta 143:Dora kur'ani akan najasa, kamar bisa jinni ko fitsari da makamantansu, koda najasar ta bushe ne,idan za;a iya cewa keta alfarmar kur;ani ce.Sannan dauke kur'anin daga bisa najsar wajibi ne.

Mas'ala ta 144:Rubuta ayar kur'ani ko da harafi daya ne daga kur;ani da tawadar da a ka yi da najasa haramun ne.Idan kuwa an riga an rubuta wajibi ne a wanke shi,ko ta hanyar goge rubutun ta yadda za'a kawar da rubutun.

Mas'ala ta 145:Ya kamata a kauce ma ba  kafiri kur'ani, sannan idan ya riga ya shiga hannun kafirirn idan zai yiwu a karbe shi, ya kamata a karbe shi daga gare shi, amma idan kafirin yana amafani da shi ne don bincike akan addinin musulunci, sanna kuma mutum ya san wannan kafirin ba najasa ba ne ko kuma hannunsa ba ya da lema, babu laifi a ba shi kur'anin.

Mas'ala ta 146:Idan takar dar kur'ani ko kuma abin da wajibi a girmama shi kamar takardar da ta ke dauke da  sunan Allah ko manzo da sauran ma'asumai a.s. idan ta fada kamar cikin najasa miasali kamar cikin masai wajibi a fito da ita kuma a wanke ta.Amma idan ba ya yiwuwa a fito da ita,to ya kamata mutum ya kaucewa amfani da wannan bayan gidan sai ya tabbatar da cewa ta zama kasa, wato ta lalace.

Mas'ala ta 147:Ci ko shan najasa haramun ne.haka ma mutum ya ba wani najasa haramun ne,amma idan yaro da kansa ya ci najasa ko hannunsa ya na da najasa ya ci abinci ba dole ba ne a hana shi.

Mas'ala ta 148: Babu laifi Sayarwa  ko ba da aron abin da ba wajibi ne ba  amfani da shi sai yana da tsarki,saboda haka ba dole ba ne ka gaya wa mai saye cewa abin yana da najasa.Amma sayar da abin da amfani da shi sai yana da tsarki, cinikin yana da inganta idan ya kasance abin zai yiwu a tsakake shi, sanan kuma dole a gaya wa mai saye cewa yana da najasa, a wannan halin babu laifi a sayar da shi ko a ba da aronsa, amma idan abin ana iya yin amfani da shi ga wani abin da ba dole ba ne sai ya zama mai tsarki ba dole ba ne a gaya ma mai saye cewa yana da najasa, sai idan mai sayarwa ya san cewa zai yi amfani ne da shi wajen abin  da sai da tsarki a ke amfani da shi.

Mas'ala ta 149:Idan mutum ya ga wani zai ci najasa ko zai yi salla da tufafin da yake da najasa ba wajibi ba ne ya gaya masa cewa suna da najasa.

Mas'ala ta 150:idan wani wuri a cikin gidan mutum ya zama mai najas kamar dardumarsa sannan t kasance mai lema kuma sai baki suka shogo gidansa ba dole ba ne ya gaya musu cewa akwai najasa a wajen.

Mas'ala ta 151:Idan mai gida yana cikin cin abinci sai ya ga najasa, to dole ne ya gaya wa bakinsa cewa akwai najasa a cikin abincin,amma idan daya daga cikin bakin ya ga najasa cikin abinci ba dole ba ne ya gaya wa sauran.

Mas'ala ta 152:Idan abin aro ya zama  mai najasa ko kuma mutum yana so ya ba wani aron wani  abu mai najasa, idan mutum ya san cewa wanda zai amshi aron zai yi  amfani da shi wajen ci ko sha wanda dole ne ya zama mai tsarki, to dole ne ya gaya masa cewa akwai najasa.

Mas'ala ta 153:Idan yaro ya zma yana iya gane abu mai kyau da marar kyau, sannan ya fadi cewa abin da ke hannunsaa yana da najasa ko ya ce na wanke wannan abin mai najasa bai kamata ba  a yarda da maganarsa.

Baya kanu Gaba