Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Abubuwan da ke tsarkake najasa:

Mas'ala ta 154:Abubuwa guda sha daya ke tsarkake najasa, sune kamar haka: Ruwa,kasa,Rana,canzawar abu zuwa wani abu,maida tsumi mai sa maye marara sa maye,Maida abu zuwa wani wuri,Musulunci,Idan uba ya musulunta yaronsa ya zama mai tsarki,gushewar najasa ga dabbobi,Istibra'in dabba mai cin najasa,fakuwar musulmi.Hukuncin  kowa ne yana zuwa daya bayan daya.

1-Ruwa:

Mas'ala ta 155:Ruwan da ya kai kur, yana tsarkake najasa tare da sharudda guda hudu.

Na daya:Ya zama ba ya da gauraye,Saboda haka ruwa mai gauraye koda ya kai yawan kur ba ya tsakake abu mai najasa.

Na biyu: ya zma mai tsarki.

Na uku: ya zama lokacin da za'a wanke abu mai najasa a cikinsa launi ko dandanonsa sakamakon najasar bai canza ba.

Na hudu:Bayan wanke abu mai najasa ya zama ba a ganin najasar acikin rowan, amma idam ruwa kadan ne bayan sharuddan da suka gabata akwai wasu sharuddan zamu fada idan mun zo wajensa.

Mas'ala ta 156:kwano ko tukunya mai najasa za a wanke ta da ruwa kadan sau uku.Amma idan ruwa mai yawa ne ko mai gudu, sau daya ya wadatar. Amma iadan kare ya lashi kwano ko ya ci wani mai ruwa cikin kwano, dole ne farko a wanke abin da kasa, wato a goge shi da  kasa ana iya sa wa  kasar ruwa kdan sai a goge abin da Karen ya ci abinci, sannan sai a wanke kwanon da ruwa sau biyu,amma idan ruwa mai yawa ne ko mai gudu sau daya ya wadatar, amma dai abin da yafi shima a wanke sau biyun.Amma idan da rowan sama ne sau daya ya wadatar. Haka ma idan yawun Karen ya zuba cikin abin cin abinci shima za'a tsarkkake shi kamar yadda muka fada a sama.

Mas'ala ta 157:Idan abin da kare ya sanwa najasa ba zai yiwu a wanke shi da kasa ba, wato bakin kwanon ko tukunyar karami ne  ta yadda ba zai yiwu ba a goge shi da kasa, to wannan abin ba zai tsarkaka ba.

Mas'ala ta 158:Amma idam alade yaci abinci a cinkin wani kwano ko tukunya, dole a wanke abin sau bakwai idan da ruwa kadan ne,Haka nan ma idan cikin rowan kur ne ko mai gudu abin ta fi shi ma a wanke sau bakwai din,amma ba dole ban e a wanke da kasa kamar yadda aka fada a sama, amma dai shi ma abin ya fi a wanke da kasar.

Mas'ala ta159:Idan za,a wanke wurin day a zma mai najasa sakamkon zuba giya da aka yi a cikinsa, sai a wanke sa sau uku idan ruwa kadan ne,amma idan ruwa mai yawa ne,amma abinya fi  a wanke sau bakwai.

Mas'ala ta 160:butar kasa wadda aka yi da yumbu mai najasa, ko kuma ruwamai najasa ya shiga a ciki,idan a ka sanya shi cikin ruwa mai gudu ko ruwa mai yawa, duk inda ruwan ya taba ya tsarkaka,amma idan ana so a wanke cikinsa dole ne a sanya shi cikin rowan kur ko mai gudu ya dade ta yadda rowan zai ratsa ko'ina, sannan ya tsarkaka.

Mas'ala ta 161:Ana tsarkake kwano mai najasa ta hanya biyu kamar haka:

Ta daya: a cika shi da ruwa sau uku,

Ta biyu:a sanuya ruwa a cikin amma gauraya shi ta yadda ko'ina a cikinsa zai samu rowan sannan a zubar.

Mas'ala ta 162:Idan tanki ko wani abu babba ya samu najasa idan aka cika shi da ruwa sau uku a ka zubar,haka nan ma idan aka zuba ruwa ta sama ta yadda ko'ina zai rowan zai iya tabawa sau uku, sannan duk lokacin da aka fitar da rowan sai wanke abin da aka fitar da ruwan.

Mas'la ta 163:Idan aka gusar da najasa daga abin dab a kwno bad a makamantansa, idan ka sanya abin cikin ruwa mai yawa kur, ko ruwaa mai gudu sau daya yana tsarkaka,amma da sharadin ruwan ya taba ko'ina.Amma abin da yafi shi ne idan ya kasance tufafi ne ko darduma sai a matse ruwan.

Mas'la ta 164:Idan ana so a wanke abin da ya samu najasa hanayar  fitsari da ruwa kadan,Idan aka zuba ruwa sau daya ta yadda ba sauran fitsarin a sama,sannan aka kara zubawa sau daya ya zama mai tsarki.Amma dai abin ya fi shi ne aka zuba ruwa sau daya wato sau biyu kenan bayan gusar da fitsarin.Sanana ba dole ban e a matse idan ya kasance tufafi ne ko darduma.

Mas'ala ta 165:Idan wani abu ya taba fitsarin yaronn da bai kai shekara biyu ba, sannan bai fara cin abinci ba, sannan bai sha nonon alade ba, idan aka zuba ruwa sau daya bisa abin ya tsarkaka.Amma mustahabbi ne a kara zuba ruwa sau daya a kai, sannan idan tufafi ne ko darduma ba dole ba ne sai matse.

Mas'ala ta166:Idan wani ya samu najasa ta hanyar wani abu bna fitsari ba,bayan gusar da najasar zuba ruwa sau daya ya wadatar.Sannan idan wankewar farko najsar ta fita ma ya wadatara,amma abin day a fi dai shi ne nidan tufafi ne ko makamancinsa sai an matse ta yadda ruwan zai fita.

Mas' ala ta 167:Idan tabarmar da aka saka da zake ta zama mai najasa, idan ka sanya ta cikin ruwa mai yawa (kur ) ko ruwa mai gudu, idan najasar ta  fita ya zama mai tsarki.

Mas'ala ta168:Idan bayan shinkafa ,alakama da sabulu da dai makamantansu  suka samu najasa Idan aka sanya su cikin ruwan kur ko mai gudu sun zama mai tsarki.Amma idan cikinsu ya samu najasa bay a tsarkakuwa.

Mas'la ta 169:Idan mutum ya yi shakka akan cewa shin najasa ta shiga cikin sabulu ko ba ta shiga ba, sai ya yi hukunci da ba ta shiga ba.

Mas'ala ta 170:Idan bayan shinkafa ko nama suka samu najasa,idan mutum ya san su cikin wani kwano ya zuba ruwa a ciki sau uku,sun tsarkaka, sannan kwanon ma ya tsarkaka.Amma idan ana so a tsarkake abin da yake bukatar a matse shi, a cikin wani kwano ko bokiti, to dole ne duk lokacin da aka wanke sai an matsae ta yadda ruwan zai fita, sannan a sake zuba wani ruwan.

Mas'ala ta171: idan tufafin da kaa rina ya zama mai najasa, idan aka sanya shi cikin ruwan kur ta yadda ruwa ya ratsa ko'ina ya tsarkaka, koda ya kasance lokacin da ake matse shi ruwan rinin ya fito.

Mas'ala ta 172:Idan aka wanke tufafi cikin ruwa mai gamsa kuka wanda ya kasance kur ne ko mai gudu,bayan an wanke sai aka ga wannan dattin ruwan bias tufafin, idan dai ba a yi tsammanin cewa ba wannan dattin ruwan ya hana ruwan ratsa tufafin, to wannan tufafin ya tsarkaka.

Mas'ala ta173:Bayan an wanke tufafi sai aka ga wani abu kamar kasa a jikinsa dan wannan kasa bat a hana ruwan ratsa tufafin ba, ya tsarkaka.Idan ruwa mai najasa ya shiga jikin kasa ko wani makamancinta bayan kasar mai tsarki ne amma cikinta najasa ce.======

Mas'ala ta 174:Dukkan abu mai najasa idan har najasar bat a  gushe ba daga gare shi, ba ya zama mai tsarki,Amma idan launi ko warin najasar bai gushe ba babu matsala.Amma idan sakamkon wannan warin mutum ya samu yakini ko ya yi zaton cewa lallai najasar bat a fita ba, to abin bai tsarkaka ba,

Mas'ala ta 175:Idan jikin mutum ya samu najasa  idan ya jikin ruwan kur ko ruwamai gudu idan najasar ta gushe jikinsa ya tsarkaka ba dole sai ya fito ya sake shiga ba.

Mas'la ta 176:Sakomakon samun najasa a cikin baki hakorin roba,asawaki da abincin da ke cikin baki bas u zama mai najasa, da zarar najasar ta gushe suma sun zama masu tsarki ba sai an wanke su ba.

Mas'ala ta 177:Idan sakamakon samun najasa aka wanke gashin kai ko na fuska,dole ne a tsane ruwan da ke cikin gashin,sai idan gashin bay a da yawa ta yadda ruwan da kansa zai fita ba tare da matse shi ba.

Mas'ala ta 178:Idan sakamakon wanke najasa a bisa jikin mutum sai gefen wurin ya samu ruwan najsar, yayin wanke wurin najasar idan ruwan ya taba wannan gefen da ruwan najasar ya taba ,shima yana tsarkaka loakcin da wurin najasar ya tsarkaka.Idan aka saka wani abu maitsarki cikin wani abu mai najasa idan aka zuba ruwa bisa duka biyun zasu zama masu tsarki, haka misali idan yatsan mutum ya samu najasa sai wajen wankewa sauran yatsunsa suka taba suma sun zama masu najasa, amma wajen wanke dayan gaba dayansu zasu tarkaka idan ba ki daya ya wanke.

Mas'la ta 179:Nama ko kitsen da suka samu najasa, kamar sauran abubuwa za'a iya wanke su da ruwa.Haka nan idan akwai maiko jikin mutum ko tufafi ta yadda ba  zai hana ruwa isa bisa jikin ko tufafin ba,idan aka wanke sun tsarkaka.

Mas'ala ta 180:Idan jikin mutum ko place>City>kanoCity>place> da makamantansu suka samu najasa, sannan sai suka samu maiko ta yadda zai hana ruwa isa bisa,lokacin da ake so a tsarkake su dole ne a kawar da maikon sannan a wanke.

Mas'ala ta 181:Abin day a samu najasa amma babu ainahin najasar akai idan aka wanke shi da ruwan fanfon da yake hade da ruwan da yawansa ya kai kur,yana tsarkake da wankewa sau daya kawai.Haka nan  idan akwai ainahin najasar a bisa sai aka wanke ta a wajen fanfo ruwan da yake zuba  sakamakon wanke ainahin najsar, idan babu wari ko launoin najasar abin da ake wankewar ya tsarakaka.Amma idan ruwan da ke zuba akwai wari ko launin najasar, dole a cigaba da zuba ruwa har ya zama babu wari ko launin najasar sannan abin da ake wankewar zai tsarkaka, kuma ruwan da ke zuba ba najasa ba  ne.

Mas'ala ta 182:Idan aka wanke wani abu da ruwa kuma aka samu yakini akan cewa ya tsarkaka, amma bayan wani lokaci sai mutum ya yi shakka akan cewa shin ainahin najasar ta fita ko bat a fita ba,Idan ya samu tabbas akan cewa ruwan ya isa wurin to abin ya tsarkaka.

Mas'ala ta 183:Idan daben simintin da ruwa yake shiga a cikin ya samu najasa, idan aka wanke shi da ruwa kadan saman ya tsarkakak amma kasan shi najasa ne.

Mas'ala ta 184:Daben da tiles ko dutse ta yadda ruwa baya iya shiga cikinsa idan ya samu najasa ana iya tsarkake sad a ruwa kadan,amma dole a zuba ruwa sama ta yadda ruwa zai yi gudu a sama.Idan wanna ruan da ka zuba da kansa ya guje wurin ya tsarkaka,amma idan sai da aka sa wani abu aka tsane shi, abin da ya fi shi ne a sake zuba ruwa a sama sannan wurin ya tsarkaka.

Mas'ala ta 185:Idan saman gishirin da yake dunkule kamar dutse ya samu najasa ana iya tsarkake shi da ruwa kadan.

Mas'ala ta 186:Idan aka yi sikari mai kwarori da sikari mai najasa ko da an sanya shi a cikin ruwan kur ko ruwa mai gudu ba tsarkaka.

Baya kanu Gaba