Kasa
Mas'ala ta 187:Kasa tana tsarkake kafa ko takalmi mai najasa tare da
sharudda biyar:
Na daya:kasar ta zama mai tsarki.
Na biyu:Kasar ta zama busassa.
Na uku:Idan tafin kafa ko takalmin da ya samu najasa ta hanayar tafiya a bisa
kasar ne ko kuma ta hanayar goga kafar ko takalmi bisa kasa najasar
ta gushe.
Na hudu:Kasar dole ne ta zama turbaya, yashi ko dutsi, amma idan ya zama
bisa wani abu kamar shinfida ne aka yi tafiya ko aka goge najasar, ba ta
tsarkaka.
Na biyar:Sanana ya zamana ta hanyar tafiya ne aka samu najasar,amma idan ta
wata hanya aka samu najasar; tsarkake ta ta hanyar tafiya bisa kasa yana da
matsala.
Mas'ala ta 188:Takalmi ko tafin kafar day a samu najasa ta hanayar
tafiya bisa kasa, ba ya zama mai tsarki ta hanyar bisa tile ko kwalta ko bisa
daben da aka yi shi da katako.
Mas'ala ta 189:Wajen tsarkake takalmi ko tafin kafar day a samu
najasa, dole a yi tafiya bisa kasa a kalla taki goma sha biayar koda kuwa
najasar ta gushe kafin tako gama sha biyar din.
Mas'ala ta 190:Bad le ban e kafa ko takalmin day a samu najasar su
zama masu lema, koda ta bushe sakamakon tafiya idan ta gushe sun tsarkaka.
Mas'ala ta 191:Bayan tafiyar da ka yi da takalmi ko tafin kafa ta
yadda suka tsarkaka gefensu ma ya tsarkaka.
Mas'ala ta 192:Wanda yake tafiya da wannu da guyawunsa(gurgu)idan
tafin hannunsa ko guyawunsa suka samu najasa, tsarkake su ta hanayar tafiya yana
da matsala.Haka nan ma kasan sanda ko kafar da ake yi ta katako ko ta roba,
takalmin garagu masu tafiya da hannun da guyawu, tayar mota ko keke, da dai
makamantansu. ba a tsarkake su ta hanayar tafiya idan suka samu najasa.
Mas'ala ta 193:Idan sakamkon tafiya aka gusar da najasa akan takalmi
ko tafin kafa, amma said dan wani abu daga najasar ya ragu amma ba iya ganinsa,
abin day a fi shi ne a yi koakri a gusar da shi duka,amma ragowar launi ko
wari babu matsala.
Mas'ala ta194:Bangaren kafa ko takalmi dab a su isa bisa kasa yayin
tafiya sakamkon yafiya ba su tsarkaka.Haka nan tsarkake kasan safa ta hanyar
tafiya ba yana da matsala,amma idan kasan safar na fata ne yana tsarkaka
sakamakon tafiya.
Rana
Mas'ala ta 195:Rana tana tsarkake kasa da gini da duk abin da baya
daukuwa kamar koaf ko taga da dai makamantansu,haka nan ma kusar da ke jikin
bango ana lissafa ta ne bangaren ginin, idan suka samu najasa rana tana tsarkake
su tare da sharudda guda shida.
Na daya:Abu mai najasar ya zama mai leman e ranar ta busar da shi,don
haka idan ya kasance busasshe yayin da rana take bugunsa bay a zama mai tsarki.
Na biyu:A kawar ainahin najasar akan abin kafin ranar na buge shi.
Na uku:Kada wani abu yak are shi daga ranar ya zama bugub ranar ne
ya busar da shi, amma idan ya zama kamar labule ko giza-giza marar kauri sukan
dan kare babu matsala.
Na hudu:Ya zamana ranar ce kawai ta busar da abin, don haka idan abin ya
bushe ne sakamakon iska tsarkinsa yana da matsala,amma idan isakan kadan
ta yadda ba za a ce shi ya busar da abin ba, ba matsala.
Na biyar:Idan kasa ko ginin da ya samu najasa ya zamana najasar ta
shiga cikinsa, idan ranar a loakci guda ta busar da shi duka,ciki da bayansa
suna tsarkaka.Amma idan a lokaci na farko kawai ranar ta busar da bayansa ne
amma cikinsa bai bushe ba, kawai bayansa ne zai zama mai tsarki.
Na shida:kada ya zama tsakanin cikin gini ko karkashin kasar da ta samu
najasa, akwai abin ya kare rana ta isa zuwa gare shi.
Mas'ala ta 196:Rana tana tarkake tabarmar da ta samu najasa, haka nan
itaciya ko ciyawar da suka sami najasa suna tsarkaka yayin da rana ta busar da
su, da sharadin ya zama babu ainahin najasar.
Mas'ala ta 197:Idan rana ta bugi kasar da take da najasa, sai mutum ya
yi shakka akan cewa shin lokacin da rana ta bugi kasar nan, shin ta kasance mai
lema ko kuwa a'a, sannan idan tana da lema shin ranar ce ta busar da ita ko
kuwa, anan hukuncinsa shi ne har yanzu akwai najasar.
Mas'ala ta198: idan rana ta bugi wani bangare na bango, bangaren da
ranar ba ta buga ba, bai tsarkaka ba.Amma idan bangon ya kasance marar kauri ta
yadda ranar ta iya busar da shi ba matsala, shima ya tsarkaka.
Canzawar najasa
Mas'ala ta 199:Idan abin da yake da najasa ya canza zuwa wani abu
daban ya zma mai tsarki.kamar katako mai najasa idan aka kona shi tokarsa
mai tsarki ce.ko kuma saka kare cikin kogin gishiri idan ya zama gishiri ya zma
mai tsarki.Amma idan abu bai canza ba zuw wanidaban bay a tsaekaka,kamar idan
alama mai najasa ta koma gari har yanzu tana nan mai najasarta.
Mas'ala ta 200:Biutar kasa wadda aka yi da kasa mai najasa ita ma
najsa ce.Don haka ya kamata a kaurace wa gawayin da aka samu da ice mai
najasa.
Mas'ala ta 201:Abu mai najasa da ake shakku akan shin ya koma wani
daban ko kuwa yana nan halinsa na da, najasa ne.
|