|
||||||||||||||||||||||
|
Hukuncin alwallar Jabira(rauni):Abin da ake daure ciwo da maganin da ke saman raunin ana kiran su jabira. Mas’ala ta 328:Idan ya kasance akan daya daga cikin gabban alwalla akwai ciwo ko rauni kamar karaya, idan ya kasance wurin yana bude kuma zuba ruwa akai ba ya cutarwa, ana dole ne a yi alwalla kamar yada ake yi idan babu ciwon. Mas’ala ta 329:Amma idan ya zamana ciwon bude yake amma zuba ruwa akan ciwon yana da cutarwa,anan sai ya wanke gefen ciwon, idan shafar ciwon da hannun mai lema bay a cutarwa, anan sai ya shafi kan ciwon da hannunsa mai lema.Ammam idan ya zamana zai cutar sai dora wani kyalle mai tsabta a sama sai ya shafe samansa.Idan ya zama wannan ma zai iya cutarwa ko saman ciwon akwai najasa ta yadda ba zai yiwu ba a shafe shi, anan sai ya wanke gefen ciwon kamar yadda ya zai wanke yayin alwalla, misali dag sama zuwa kasa, amma anan ihtiyati wajib sai ya hada da taimama. Mas’ala ta 330:Idan ya kasance ciwon yana gaban kai ne ko bias kafa,sannan a bude yake, sannan ba ya yiwuwa ya shafi samansa, anan sai ya dora wani kyalle sannan ya shafi samansa.idan kuwa ba zai yiwu bay a dora kyallen anan ba dole ban e ya yi shfar, amma dole ne bayana alwallar ya hada da taimama. Mas’ala ta 331:Idan ya zamana a kan ciwo akwai wani abu da ak daure ciwon ko karayar, sannan kuma zai yiwu a bude shi kuma babu wata matsala, sannan ruwa ba zai cutar ba,anan dole ne ya bude shi sannan ya yi alwalla,wannan ciwon kuwa ko da ya kasance bisa fuska ne ko kafa ba bambanci. Mas’ala ta 332:Idan ya kasance ciwo yana kan fuska ne ko kafa, sannan bude shi ba zai zama matsala ba, sai dai zuba ruwa akai zai iya cutarwa, amma shafarsa da hannu mai lema ba zai cutar ba,anan dole ne a yi shafar. Mas’ala ta 333:Idan ya zamana ba zai yiwu ba a bude ciwon.amma ciwon da abin da aka daure ciwon ba su da najasa, sannan zai yiwu a zuba ruwa akan ciwon ta yadda ba zai cutar ba kuma babu wata wahalarwa,anan dole ne a zuba ruwa akan ciwon.Amma idan ciwon ko abin da aka aza akan ciwon yana da najasa, idan ya zamana isar da ruwa akan ciwon babu wata wahala, anan dole ne a isar da ruwan akan ciwon.Amma idan ruwan zai cutar ko kuma ba zai yiwu ba a isar da ruwa akan ciwon, ko kuma ciwon akwai najasa kuma ba zai yiwu ba a wanke shi ta yadda za a iya wanke shi kamar yadda aka fada a wajen alwalla, idan ya zamana abin da aka daure ciwon ko kuma maganin da ke kan ciwon ba ya da najasa,anan sai a shafi kan ciwon.Amma idan suna da najasa ko ba zai yiwu ba a shafi saman ciwon da lema kamar idan akwai magani a saman ciwon, anan sai a dora wani kyalle mai tsabta a yi shafar a kai.Amma idan wannan ma ba zai yiwu ba sai a yi taimama bayan alwallar. Mas’ala ta 334:Idan ya zmana jabira ta cika dukkan fuska ko daya daga cikin gabban alwalla, anan hukuncin da muka fada na alwallar jabira ya wadatar kuma alwallar jabirar ta wadatar,amma idan jabirar ta rufe fiye da gabban alwalla, anan alwallar jabira ba ta wadatarwa,anan dole ne a yi taimama. Mas’ala ta 335:Wanda yake da jabira a tafin hannu da kan ‘yan yatsu,idan ya shafi wajen da hannu mai lema yayin alwalla yana iya shafar kai da kafafunsa da wannan lemar.kuma yana iya shafar da wasu sassan hannunsa inda lema take. Mas’ala ta 336:Idan ya kasance jabira ta mamaye dukkan kafa amma akwai wurin da yake bude akan yatsu da saman kafar,anan dole ne ya shafi wurin da yake bude sannan inda yake da jabira sai ya shafin saman jabirar. Mas’ala ta 337:Idan ya kasance akwai jabira da yawa akan fuska da hannuwa,anan dole ne ya wanke wuraren da babu jabirar,amma idan jabira ta kasance bisa kai ko kafafu,idan akwai wurin da ya wajaba a shafa a bude,anan sai a shafi wannan wurin,amma sauran da yake da jabira sai a yi aiki da hukuncin alwallar jabira. Mas’ala ta 338:Idan ya kasance jabira tana da yawa ta yadda ta mamaye wurin da ya wuce misali sannan kuma ba zai yiwu ba a cire ta, anan sai mutum ya yi aiki da hukuncin alwallar jabira, sannan akan ihtiyati ya yi taimama,ammam idan zai yiwu acire jabirar anan dole ne a cire ta.Idan ya zamana ciwon yana kan fuska ne ko hannaye,sai a wanke gefen jabirar,idan kuwa ya kasance bisa kai ne ko kafafusai a shafi gefenta,sai a yi amfani da hukncin jabira a wurin da ciwon yake. Mas’ala ta 339:Idan ya kasance babu ciwo ko karaya akn gabban alwalla,amma saboda wani dalili ruwa zai cutar da fuska da hannaye,anan dole ne mutum ya yi taimama,amma ihtiyat wajib idan ya zamana wani wuri ne daga cikin fuska ko hannaye ruwan zai iya cutarwa,sai a wanke gefensa, sannan ayi taimama. Mas’ala ta 340:Idan mutum ya ji ciwo a kan daya daga cikin gabban alwalla ta yadda ba zai yiwu ba ya wanke wajen da ruwa ko kuma ruwa zai ya cutar da wurin,idan wajen yana rufe ne, dole ne ya yi aiki da hukuncin jabira anan,idan kuwa yana bude ne ihtiyat wajb shi ne ya dora wani kyalle a kai sai ya shafi sama da lemar da ke kan hannunsa. Mas’ala ta 341: idan ya zamana akwai wani abu ya like akan gabban alwalla ko wankata yadda kuma ba zai yiwu ba a cire shi, ko kuma cire shi yana da wuya ta yadda ba za’a iya daure ma hakan ba,anan dole ne a yi aiki da hukuncin jabira. Mas’ala ta 342:Wankan Jabira kamar alwallar jabira yake,amma ihtiyat wajib shi ne, a yi shi a jere ba irtimasi ba(zamu yi bayanin irtimasi a cikin wankan janaba). Mas’ala ta 343:Wanda ya kasance taimama ce ta hau kansa,idan ya zamana daya daga cikin gabban alwallarsa yana da ciwo ko karaya,anan sai ya yi aiki da hukuncin alwallar jabira ya yi taimama ta jabira. Mas’ala ta 344:Wanda ya kasance da alwalla ko wankan jabira zai yi salla,idan ya san cewa har zuwa karshen lokaci matsalarsa ba za ta gushe ba,yana iya aiwatar da sallarsa tun farkon lokaci.Amma idan yana sa ran cewa zata iya gushewa zuwa karshen lokaci ihtiyat wajib shi ne ya yi hakuri zuwa karshen lokacin sai ya gabatar da wankan ko alwallar, idan kuwa matsalar bat a kau ba sai ya yi alwallar jabrar ya yi sallarsa. Mas’ala ta 345:Wanda bai san cewa ba shin dole ne ya yi taimama ko kuwa alwallar jabira , anan ihtiyat wajib shi ne ya gabatar da duka biyun. Mas’ala ta 346:Salloliln da mutum ya yi da alwalla jabira sallarsa ta inganta, sannan yana iya yin wsu sallolin da wannan alwallar ko da kuwa uzirinsa ya gushe.Amma a wurin da bai san wane abu ne yah au kansa alwallar jabira ko taimama, anan idan uzirinsa ya kau dole ne ya sake alwalla don yin salloli na gaba.
|