|
||||||||||||||||||||||
|
Wankan wajibi:Wankan wajibi ya kasu zuwa gida bakwai:1-wankan janaba,2-wanakan haila,3-wankan biki(haihuwa)4-wankan istihala,5-wankan taba gawa,6-wankan gawa,7-wanka da mutum ya yi rantsuwa cewa zai yi ko ya yi bakance. Hukuncin Janaba: Mas’ala ta 347:Mutum yana samu janaba ta hanya biyu: Ta daya: ta hanayar jima’i Ta biyu: ta hanyar fitar maniyyi, wannan kuwa a cikin barci ne ko a farke, cikin son ran mutum ko ba cikin sonsa ba, kadan ne ko da yawa da sha’awa ne ko ba da sha’awa ba. Mas’ala ta 348:Idan wata lema ta fito daga mutum sannan bai sani ba shin maniyyi ne ko fitsari ko kuwa wani abi ne daban,sannan kuma ya fito tare da sha’a kuma da karfi,sannan bayan fitowarsa sai jikin mutum ya mutu,wannan lemar za’a yi mata hukuncin maniyyi ne,amma idan babu wadanannan siffofi ko kuma babu daya daga ciki, wannan lemar ba ta da hukuncin maniyyi.Amma wajen mace da marar lafiya ba dole ba ne sai ya kasance ya fito da karfi,idan ya fito ne sakamkon sha’awa ba dole ba ne sai ta ji jikinta ya mutu. Mas’ala ta 349:mustahabbi ne mutum ya yi fitsari bayan fitar maniyyi.Amma idan bai yi fitsari ba bayan ya yi wanka sai ya ji wata lema ta fito daga gare shi wadda bai sani ba shin maniyyi ne ko wani abin daban, anan zai hukunci da cewa maniyyi ne. Mas’ala ta 350:Idan mutum ya yi jima’i kuma hashafarsa ta faku(wurin da ake yin kaciya)da mace ne ya yi jima’i ko da namiji, ta gaba ne ko ta baya,baligi ne ko ba baligi ba, koda maniyyi bai fito ba dukan su biyu janaba ta kama su. Mas’ala ta 351:Idan mutum ya yi shakka akan cewa shin da ya yin jima’i hashafa ta faku ko kuwa bata faku ba, anan janaba ba ta kama shi ba. Mas’ala ta 352:Idan mutum ya sadu da dabba wa’iyazu billah,sannan maniyyi ya fita daga gare shi anan idan ya yi wanka ba sai ya yi alwalla ba,yana iya yin salla da wannan wankan,haka nan idan maniyyi bai fito ba amma kafin ya sadu da dabbar yana da alwalla, shi ma ba sai ya yi alwalla ba idan ya yi wanka ya wadatar,amma idan ba shi da alwalla dole ne sai ya yi alwalla sannan ya yi salla. Mas’ala ta 353:Idan maniyyi ya motsa amma sai bai fito ba, ko kuwa mutum ya yi shakka akan cewa shin ya fito waje ko bai fito ba,anan wanka bai wajaba a kansa ba. Mas’ala ta 354:Wanda ba ya iya yin wanka, amma yana iya yin taimama, idan lokacin salla ya riga ya shiga, bai kamata ba ya sadu da iyalinsa ba, ba tare da wata bukatar hakan ba, amma idan ya zamana saboda jin dadi ko kuma tsoron kada ya aikata wani laifi, babu laifi. Mas’ala ta 355:Idan mutum ya ga maniyyi a bisa tufafinsa, sannan ya san cewa daga gare shi yake,Sannan kuma bai yi wanka ba sakamakon hakan,anan dole ne ya yi wanka sannan ya ramma sallolin da yake da yakini bayan fitowar maniyyin ba tare da wanka ba ya yi su.Amma sallolin da ba ya da tabbas a kan hakan ba dole ba ne ya rama su.
|