Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Abubuwan da suka haramta ga mai janaba:

Mas’ala ta 356: Abubuwa guda biyar ne suka haramta  ga mai janaba ya aikata su:

Na Daya: Taba rubutun kur’ani ko sunan Allah madaukaki, Hakanan sunayen annabawa da Ma’asumai a.s. a matsayin Ihtiyat wajib.

Na biyu:Shiga cikin masallaci mai alfarma wato masallacin Makka da na madina, koda gittawa ta ciki ne a wuce.

Na uku:Tsayuwa a cikin sauran masallatai, amma idan da nufn gittawa ne ta ciki a wuce babu matsala, Haka nan  idan mutum ya ajiye wani abu a ciki yana so ya dauko shima babu laifi.Haka a kan ihtiyat shima bai kamata ba ya tsaya a cikin haramin Imamai a .s. duk da cewa ya kamata a kiyaye hukuncin masallacin manzo a wajen haramin Ma’asumai a.s.

Na  hudu:Ajiye wani abu a cikin Masallaci.

Na biyar:Karanta daya daga cikin surorin da suke da sujjada ta wajibi,wadan nan surori kuwa guda hudu ne:Sura ta 32 TAnzil,sura ta 41 suratus sajada, surar ta 53 suratun najm, sai sura ta 96 suratul alaq(ikra’a) idan mutum ya karanta koda harafi daya na wadan nan surorin haramun ne.

Abubuwan da suke makaruhi ga mai Janaba:

Mas’ala ta 357:Abubuwa tara ne suke makaruhi ga mai Janaba:

Na daya da na biyu:ci da sha amma idan mutum ya yi alwalla ba laifi.

Na uku:Karanta fiye da aya bakwai daga surorin da babu sujja ta wajibi a cikinsu.

Na hudu:Taba gefe tsakanin  rubutun kur’ani.

Na biyar:Daukar kur’ani.

Na shida:barci da Janaba, amma idan mutum ya yi alwalla babu laifi,haka nan idan babu ruwa mutum yana iya yin taimama.

Na bakwai:yin kunshi da makamantan wannan .

Na takwas:shafa mai ga jiki.

Na tara:yin jima’i bayan mutum ya yi mafarki ya fitar da maniyyi.

Wankan Janaba:

Mas’ala ta 358:wankan janaba shi da kansa  mustahabbi ne, amma ayan zama wajibi sakamakon aikata wasu ayyuka kamar sallar wajibi.Amma don yin sallar gawa ba ya wajaba.haka nan wajen yin sujjada shukur da sujjadar karatun kur’ani,wanka ba ya wajaba.

Mas’ala ta 359:Ba doleba ne yayin wanka mutum ya  yi niyya cewa zai yi wanka wajibi ko na mustahabbi.Idan kawai mutum ya yi niyyar kusanci ga Ubangiji ya wadatar, wato da ma’anar aikata aumurnin Allah T.A.

Mas’ala ta 360:Ana yin wanka ta hanyoyi guda biyu ya kasance na wajibi ne ko na mustahabbi.wadan nan hanyoyi guda biyu kuwa sune kamar haka, Irtimasi wato mutum ya tsunduma cikin ruwa mai yawa gaban dayan jikinsa ya shige a cikin ruwan,sanan sai tartibi wanda mutm zai wanke kaizuwa kafadu sannan sai ya wanke bangare dama sannan ya wanke bangaren hagu.

Baya kanu Gaba